
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yace a shirye yake sama da kowanne lokaci don Jagorantar hadakar Jam’iyyun Hamayyar Najeriya.
Atiku ya sanar da haka ne cikin sakon Taya murna da ya aikewa gwamnonin PDP da NNPP bisa nasarar da suka samu a kotun koli.
Atiku yace ”Hukunce-hukuncenkotun koli na yau nasara ce ga al’ummar jihohin Bauchi Da Fulato da Akwa Ibom da Zamfara Kuma babbar nasara ce ga Dimukuradiyya ta hakika.
”Ina Kuma Mika sakon Taya murna ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bisa gagarumar nasarar da ya samu a kotun koli”.
Yace Wannan lokacin zai bada gagarumar dama ta sake nanata manufat sa ta Samar da tsagin adawa Mai karsashi domin inganta Dimukuradiyya a Najeriya.
”Yanzu a shirye na ke na jagorancin wannan gwagwarmayar sama da kowanne lokaci, domin aiki tare da gwamnonin mu da sauran shugabannin domin Samar da kyakkyawaar makoma ga kasar mu.”
Yace Hukuncin na kotun koli ya bada tabbacin ci gaba da samun Ingantaccen tsarin shugabancin da PDP ta kafa a wadannan jihohi.
”Ina kira ga gwamna Bala Muhammad na Bauchi da Dauda Lawan na Zamfara da Caleb Muftwang na Fulato da kuma Umo Eno na Akwai Ibom su Kalli nasarar da suka samu a Matsayin dama da suka samu ta ci gaba da shimfida ayyukan raya kasa da suke.”
”A yanzu mun wuce lokacin zabe, Kuma Ina da yakini yanzu PDP zata mayar da hankali kan nauyin Dake kan ta a Matsayin ta babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya karkashin kulawar gwamnonin ta da ni Kai na.”