Kotun koli ta tabbatar da hukuncin shekara biyar da aka yanke wa tsohon ɗan majalisar wakilai Farouk Lawan bisa samun sa da laifin karɓar cin hancin na kuɗi dala 500,000 daga hannun dan kasuwa Femi Otedola, shugaban kamfanin Zenon Petroleum and Gas Limited
Ƙarar da aka ɗaukaka ta buƙaci a soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yanke a ranar 24 ga Fabrairu, 2022, inda ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari tare da wanke shi a kan tuhume-tuhume biyu daga cikin ukun da aka gurfanar da shi a kai, waɗanda suka shafi cin hanci da rashawa.
A hukuncin da mai shari’a John Okoro ya shirya amma mai shari’a Tijjani Abubakar ya karanta, kotun kolin ta ce ƙarar da Lawan ya shigar ba ta da cancantar da za a saurare ta sannan ya yi watsi da ita.
Tawagar masu yanke hukuncin da ta ƙunshi alƙalai biyar gaba ɗaya sun tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a shekarar 2022 wanda ya tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Lawan na shekaru biyar dangane da tuhume-tuhume uku da ake yi masa.