Aure da Karatu ba ya taɓa zamowa Mace ƙalubale a rayuwa – Dr. Maimuna

0
662

Mafi yawa daga Mata na ganin babban ƙalubale ne ga Mace, a lokacin da ta haɗa karatu da kuma zaman aure lokaci guda. Sai dai Dakta Maimuna na ɗaya daga cikin matan auren da suke ƙoƙarin wayar da kan ‘yan uwansu Mata akan muhimmancin yin karatu ko da kuwa su na da aure ne.

Maimuna wacce ta ke koyarwa a jami’ar tarayya da ke Dutse ta jihar Jigawa, ta bayyana cewar tasirin da ilimi ya ke ga rayuwar Mace, musamman matar aure ba ƙarami ba ne.


Ta bayyana hakanne a lokacin tattaunawa da ita a gidan rediyon Freedom da ke Kano.

Malama Maimuna ta yi karatunta ne a ɓangaren ilimin ƙwayoyin halitta. Kuma tun daga digirinta na farko har zuwa na uku, ta yi nazari ne da bincike akan cututtukan da ake kamuwa da su ta fuskoki da dama a zamantakewarmu.

Ta kuma bayyana cewar wani littafi da ta rubuta akan muhimmancin dawo da aikin duba-gari cikin al’umma zai taimaka matuƙa gaya don kyautatuwar muhalli da kuma samun ingantacciyar lafiya.

A tattaunawar ta su, ta yi kira ga mata da su dena ganin haɗa aure da karatu a matsayin wani ƙalubale. Domin kuwa duk abin da Mace ta ƙudurci aniyar yi, madamar ta shirya akan sa, to za ta yi nasara.

Dakta Maimuna dai ta yi rubutun digirinta na farko akan cutukan da ake ɗauka akan injin cirar kuɗi, na biyu kuma akan cutukan da suke kama mafitsara, na ƙarshe digirin-digirgir ta yi shi ne akan amfanin Kuka wajen dakatar da gudawa ga ƙananan yara.

Malama Maimuna ‘yar asalin Kano ce, ta na da aure da kuma yaranta guda uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here