Muhammadu Abubakar Rimi: Gwarzon ɗan siyasa ya cika shekaru 14 da rasuwa

0
322

A ranar 4 ga watan Aprilun shekarar 2010 kimanin shekaru 14 da su ka gabata dubban daruruwan mutane ne suka halarci jana’izar gwamnan tsohuwar Jihar Kano na farar hula na farko, Alhaji Muhammad Abubakar Rimi, wanda ya rasu sakamakon cutar hawan jini.

Ciwon ya taso masa ne baya da ‘yan fashi suka tare su a garin Darki, yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Kano daga jihar Bauchi.

Jama’ar da suka halarci jana’izar tasa sun hada da shugabannin gwamnatoci, da sarakuna, da malaman addini, da ‘yan siyasa da kuma dimbin jama’a.

Na’ibin Limamain Kano Malam Nazifi Dalhatu ne ya jagoranci sallar, bayan an shafe kimanin sa’o’i uku ana jiran isa da gawar fadar mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, inda aka yi jana’izar.

Mutuwar ta sa ta ruda jama’a da dama a jihar Kano, musamman ma masoyansa, duba da yadda ya baiwa jihar muhimmiyar gudunmawa lokacin da yake mulkin a shekarar 1979 zuwa 1983.

Wanene Muhammad Abubakar Rimi?

An haifi Alhaji Abubakar Rimi a shekarar 1940 a garin Rimi ne da ke cikin ƙaramar hukumar Sumaila. Ya halarci makarantu daban daban a Nigeria da kasashen ketare inda har yayi digiri na biyu a fannin hulda da kasashen ketare.

Babban kirarin da ake yi wa Alhaji Abubakar Rimi dai shi ne limamin canji.

Wasu na ganin hakan ba zai rasa nasaba da irin yunkurin sa na samawarwa da talakan Nigeria yanci ba.

Ana kuma yaba wa marigayin da irin jajircewar da kuma kalubalantar shugabannin akan lallai sai an tabbatar da tsarin Dimokradiyya na gaskiya.

Gwagwarmaya Siyasa

Zaɓen da aka gudanar a ranar 28 ga watan Yuli na shekarar 1979 (28 July, 1979), shi ya tabbatar da shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano na farko, kuma gwamna na huɗu a jihar. An rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1979 (1 October, 1979).

Haka kuma marigayi Abubakar Rimi ya ajiye mukaminsa na gwamnan Kano a shekarar 1983, bayan ya fita daga jam’iyyar PRP sakamakon sabani da shugabannin jam’iyyar inda ya koma jami’yyar NPP.

Marigayi Abubakar Rimi ya jima yana gwagwarmaya a fagen siyasar Nigeria, inda har ana ga yana daga ‘yan gabadai gabadai da suka tallata Chief MKO Abiola kuma ya samu karbuwa da kuma nasara a zaben 12 ga watan Yulin 1992.

Alhaji Abubakar Rimi ya kuma yi takarar shugabancin Nigeria karkashin jam’iyyar PDP.

Rimi ya zama ministan sadarwa na Nigeria a shekarar 1993, sannan daga baya kuma aka nada shi shugaban bankin manoma a dai wannan shekara.

Marigayi Rimi na daga wadanda suka kafa jam’iyyar PDP, sai dai ya fice daga jam’iyyar yayinda sabani yayi kamari tsakaninsu da bangaren tshon shugaban kasar Obasanjo, inda ya koma jam’iyyar adawa ta AC.

Sai dai daga baya ya sake komawa jam’iyyar ta PDP a shekarar 2007.

Muhammad Abubakr Rimi na daga manyan jigajigan jam’iyyar PDP a jihar Kano, inda yake babban mai fada a ji a bangaren Garkuwa na jam’iyyar.

A watan Junairun 2006 wasu mutane sun haura gidansa suka kashe mai dakinsa Hajiya Sa’adatu Rimi.

Ya mutu ya bar mata daya da yaya takwas da kuma ‘yan uwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here